Majalisar Dinkin Duniya ta amince da a dauki matakan da suka dace wajen yakar mayakan jahadin kasar Iraki
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudiri ladabtarwa bisa yadda mayakann jahadi muslincin ke ci gaba da samun nasarar mamaye kasar Iraki, inda kasar Amruka ta ke ci gaba da kai hare haren soja a kan mayakan jahadin, da aka zarga da kai wani sabon hari kan yan kabilar Yazidi marasa rinjaye a yankin arewacin Iraki
Daga karshen dai a nasa bangaren Farayi Ministan kasar Iraki Nuri Almaliki ya mika wuya , tare da amincewa ya sauka daga kan mukamin bisa matsin lambar kasashen duniya.
Har ila yau Nuri Almaliki ya yi fatan ganin sabuwar gwamnatin da za a kafa a kasar, zata iya kawo karshen ci gaba da samun nasarar da mayakan jahadi ke yi yanzu haka a kasar ta Iraki
A dai gefen kuma ministocin harakokin wajen Kungiyar Tarayyar Turai a jiya juma’a sun cimma matsaya wajen baiwa yan kabilar kurdawan kasar Iraki makamai domin kare kansu daga yaki da mujahidan dake son kafa kasar musulunci tsakanin kan iayakar kasashen Irak da Syriya suka kai masu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu