Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Isra’ila zata ci gaba da kai farmaki a Gaza

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyhu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyhu AFP PHOTO / JACK GUEZ
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 min

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya shaidawa ministocinsa cewa Sojojin kasar zasu ci gaba da kai farmaki a Gaza har sai an samu tabbataccen tsaro a kudancin Isra’ila daga hare haren rokoki da Mayakan Hamas ke ci gaba da harbawa a yankin.

Talla

A yau Lahadi wasu hare haren da Isra’ila ta kai da jiragen sama sun kashe wata Uwa da yara kanana guda uku, da kuma wani babban Jami’in kungiyar Hamas Mohammed al Ghul, a kwana na 48 da Isra’ila ke luguden wuta a Zirin Gaza.

Falasdinawa kimanin 2,100 ne yawancinsu fararen hula Isra’ila ta kashe tun kaddamar da sabon rikicin a ranar 8 ga watan Yuli a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.