Malaysia

Kamfanin jirgin Malaysia zai kori Ma’aikatansa

jiragen  Malaysia Airlines a Kuala Lumpur
jiragen Malaysia Airlines a Kuala Lumpur REUTERS/Edgar Su

Kamfanin Jirgin sama na kasar Malaysia ya fitar da sanarwar korar dubban ma’aikatansa tare da sauya shugabannin da ke jagorantar tafiyar da kamfanin domin samun makoma mai kyau sakamakon jiragen kamfanin guda biyu da suka yi hadari.

Talla

Mahukuntan da ke kula da sha’anin Kamfanin sun ce zasu dauki matakan ne domin farfado da kasuwar kamfanin.

Amma hakan ba zai sa a sauya wa Kamfanin suna ba bayan bacewar Jirgi sama mai suna MH370 wanda ya taso daga Kuala Lumpur zuwa Beijing da kuma tarwatsewar jirgi MH17 a gabacin Ukraine.

Kamfanin yace zai kori Ma’aikata kimanin 6,000, kusan kashi 30 daga cikin ma’aikatansa, tare da canza shugabannin tafiyar da ayyukan Kamfanin.

Hukumar zirga-zirgar Jiragen sama ta duniya tace zata dauki matakan kare aukuwar hadarin Jirage bayan faduwar Jirage guda uku da suka yi sanadin mutuwar mutane 460 a cikin ‘yan kwanakin nan.

A ranar 17 ga watan Yuli ne jirgin Malaysia ya yi hadari a gabacin Ukraine, inda ake zargin ‘Yan tawayen kasar ne suka harbo jirgin mai dauke da mutane 298.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI