Hong Kong

China ta dora alhakin zanga-zangar Hong Kong ga makircin Amurka

香港青年人10月1日晚在港府办公大楼前示威
香港青年人10月1日晚在港府办公大楼前示威 路透社

Masu zanga-zanga a Hong Kong sun matsa akan cewar lokaci ya yi da ya kamata shugaban yankin ya sauka daga kan mukaminsa, a yayin da kasar China ke yiwa Amurka kashedin cewar ta daina yi mata katsalandam cikin harkokin cikin gidanta, da kuma yiwa mutanen Hong Kong ingiza-mai-Kantu-Ruwa

Talla

Kusan dai wannan ne karon farko da kasar China ta bayyana a fili cewar ta lura duk abinda ke faruwa a Hong Kong kitse-kiten kasar Amueka ne, harma ta nuna Yatsa ga kasar ta Amurka cewar Ahir kar ta kara.

Ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi ya fadawa Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a birnin Washington DC cewar sun gano makircin da suke kulla masu.

Ya fadi wannan a wani taron manema labarai inda yake nanatawa cewar abinda ya shafi Hong Kong harkokin cikin gidan China ne, ban a Amurka ba, kuma ya zama wajibi dukkanin kassahe su mutunta kasar China akan hakan.

Kwanaki 4 kenan ana gudanar da zanga-zangar da ta hada Mutane 4000, da suka mamaye babbar mahadar Hanyoyi da ke Taipei, a yyain da a London na kasar Burtaniya ma wasu 2000 sun mamaye Ofishin jakadancin kasar China.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.