Yemen

Harin kunar bakin Wake ya hallaka mutane kusan 50 a Yemen

Les rebelles shiites combattent l'armée yéménite à Sanaa, le 21 septembre 2014.
Les rebelles shiites combattent l'armée yéménite à Sanaa, le 21 septembre 2014. REUTERS/Khaled Abdullah

Da sanyin safiyar yau ne wani harin da dan kunar bakin Wake ya kai a Yemen ya hallaka akalla mabiya Shi’a 43 a babban birnin kasar

Talla

Baya ga wadanda suka mutu akwai kuma wasu masu dimbin yawa da suka samu munanan raunuka, kamar yanda wani gidan Talabijin mai alaka da ‘yan tawayen kasar ya sanar.

Wata majiya dai ta tabbatar da cewar a karon farko harin ya hallaka mutane 21 ne kai tsaye, a yayin da ya bar wasu Gommai a cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Daga bisani ne alkalumman yawan matattun ke ci gaba da karuwa inda ya zuwa yanzu kusan mutane 50 ne aka ce sun mutu.

Wannan harin dai na zuwa ne a bayan da aka bada labarin cewa Sabon Firaiministan kasar Yemen Ahmed Awad Bin Mubarak ya ajiye mukaminsa sakamakon sukan da mayaka ‘yan shi’a suka yi bayan kutsa kai da suka yi a babban birnin kasar wato Sana’a tun ranar 21 ga watan jiya.

A nashi bangaren Shugaban kasar Abdulrabuh Mansur Hadi tuni da ya amince da watsi da aikin da Firaiministan ya yi, a yyain da ‘Yan tawayen kasar da suka kunshi ‘yan tawayen Huthi da aka sansu da ‘yan Ansarullah sun amince su jingine boren da suka shirya yi yau Alhamis.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.