Syria

Ana tafka fada a garin Kobane dake cikin kasar Syriya

Hayakin fadan da ake tabkawa a Kobane na kasar Syriya
Hayakin fadan da ake tabkawa a Kobane na kasar Syriya REUTERS/Umit Bektas

Kungiyar mujahidan ISIS a kasar Syriya a jiya assabar ta yi ta jidali a yankuna da daman na birnin Kobane dake Syriya, a yayin da mayakan kurdawa suma suka tunkari dakarun nata wajen haifar masu da tarnaki

Talla

Majalisar DD ta bayyana matukar damuwarta kan makomar rayukan fararen hula a wannan yanki da ake tafka fada a cikinsa

Rahotannin daga kungiyar nan mai zura ido tare da fafatukar kare hakkin dan adam ta kasar Syriya, OSDH, sun bayyana cewa, dakarun kurdawa da basu da yawa sosai, kana basu da wadatacin makamai, sun yi nasarar haifar da tarnaki ga mayakan na ISIS, inda suka tilasta masu komawa baya, tare da kashe 23 daga cikinsu a yayin da suka jikkata wasu da dama
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.