Saudiya-Amurka

Wani tsohon jami'in wani kamfanin tsaron Amruka mai zaman kansa ya hallaka wani ba'amuruke a Saudiya

Le roi Abdallah ben Abdelaziz al-Saoud d'Arabie Saoudite reçoit le secrétaire d'Etat américain John Kerry, au Palais royal de Djeddah, le 11 septembre 2014.  r
Le roi Abdallah ben Abdelaziz al-Saoud d'Arabie Saoudite reçoit le secrétaire d'Etat américain John Kerry, au Palais royal de Djeddah, le 11 septembre 2014. r REUTERS/Brendan Smialowski/Pool

Hukomomi a kasar Saudiyya sun ce mutumin da ya kai wa wasu amurkawa hari har ma ya kashe daya daga cikinsu, tsohon jami’I ne a wani kamfanin samar da tsaro na Amurka da ke kasar ta Saudiyya.

Talla

Jami’in da ya kai harin mai suna Abdul Aziz Fahad Alrashid mai shekaru 24 a duniya, yana daya daga cikin ma’aikatan kamfanin na Amurkawa da aka kora daga aiki a cikin kwanakin da suka gabata saboda matsalar shaye-shaye.

Wannan irin al’amari da ya wakana dai ba asafai ake smunsa a  kasar ta Saudiya ba, sai dai kuma lura da yadda kasar ke ci gaba da saka kanta bayan kasar Amruka da kawayenta, musaman yaki da kungiyoyin dake da zafin kishin Islama irin su ISIS a kasashen Iraki da Syriya, ya sa wasu yan kasar da ke adawa da hakan na yi mata wani irin kallo cike da bacin rai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.