Iraq-Syria

Mayakan ISIL sun yi wa 'yan kabilar Yazidi kawanya a Iraqi

Wasu yara 'yan kabilar Yazidi dake gudun hijira
Wasu yara 'yan kabilar Yazidi dake gudun hijira

Rahotanni daga kasar Iraki na cewa mayakan jihadi na kungiyar ISIL sun sake yi wa larabawa ‘yan kabilar Yazidi da ke zaune a cikin yankin nan mai tsaunuka na Sinjar kawanya. Yankin na Sinjar na daga cikin na farko-farko da mayakan masu da’awar jihadi suka soma mamayewa, kafin sojojin kasashen duniya su fatattake su.Ita kuwa majalisar dokokin yankin Kurdawa mai cin gashin kanta a karkashin kasar Iraki, ta jefa kuri’ar amincewa da tura sojojin yankin zuwa Syria, domin kare ‘yan uwansu Kurdawa ‘yan Kobani, wadanda mayakan jihadin suka yi wa kofar rago yau fiye da wata daya kenan.A halin da ake ciki kuma, hare haren da sojojin kawance da Amurka ke jagoranta kan mayakan jihadi na IS, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 553 da suka hada da mayakan da kuma fararen hula.Wata kungiyar kare hakkokin bil Adama dake kasar Britania amma kuma take sa ido kan wannan yaki, ta ce mamata 464 mayakan da ke da’awar jihadin ne, sai wasu magoya bayan al-Qa’ida su 57, da kuma wasu mayakan da aka ce sun fito ne daga wata kungiya da ake kira An-nusra suka mutu.Ita kuwa majalisar dokokin yankin Kurdawa mai cin gashin kanta a karkashin kasar Iraki, ta jefa kuri’ar amincewa da tura sojojin yankin zuwa Syria domin kare ‘yan uwansu Kurdawan Kobani, wadanda mayakan jihadin suka yi wa kofar rago yau fiye da wata daya kenan.