Turkiya-Syria

Kobane: 'Yan tawayen Syria za su ratsa ta Turkiya

Kurdawan da ke rayuwa a Kobane.
Kurdawan da ke rayuwa a Kobane. AFP PHOTO/BULENT KILIC

Gwamnatin kasar Turkiya ta amince Dakarun Kurdawa su ratsa ta cikin kasarta domin kare garin Kobane daga hare haren Mayakan IS da suka yi wa garin Kawanya. Mayakan zasu hadu da ‘Yan tawayen Syria da ke yakar Gwamnatin Bashar Al Assad.

Talla

Shugaban Turkiya Reccep Tayyip Erdogan ne ya amince da matakin ba Mayakandamar ratsawa ta cikin Turkiya domin haduwa da 'Yan tawayen Syria don kare garin Kobani da Mayakan IS suka yi wa Kawanya.

Tuni gwamnatin Kurdawa ta Iraqi ta amince ta tura dakaru 200 bayan Turkiya ta amince su ratsa ta cikin kasarta.

Kuma shugaba Erdogan na Turkiya yace dakarun na Kurdawa zasu hadu da Mayakan Syria 1,300 domin yakar Mayakan IS da suke gwagwarmayar tabbatar da daular da suka kafa a yankunan da suke mamaye a kasashen Syria da Iraqi.

Erdogan dai ya amince da bukatar ba mayakan damar ratsawa cikin Turkiya ne bayan tattaunawa da Shugaba Obama na Amurka da ke jagorantar yaki da Mayakan IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.