Iran

An zartar wa wata Mata hukuncin Rataya a Iran

REYHANEH JABBARI  da aka rataye a Iran
REYHANEH JABBARI da aka rataye a Iran

Kasar Iran ta rataye wata Mata da ta kashe wani Jami’in leken asiri wanda ta yi ikirarin ya yi kokarin yin lalata da ita. Da asuba ne aka zartar wa matar mai suna Rayhaneh Jabbari da hukuncin rataya.

Talla

Iran dai ta yi watsi da kiranye kiranyen kasashen yammaci da suka kalubalanci hukuncin.
A cikin wani sako a shafin Facebook dauke da hoton Jabbari, Kungiyar Amnesty International ta yi Allah wadai da hukuncin.

A 2007 ne Jabbari da ke sana’ar dinki ta kashe Morteza Abdolali Sarbandi.

Bisa tsarin Shari’ar Musulunci kuma, an shafe tsawon shekaru biyar bangaren Shari’a a Iran yana neman dangin Sarbandi su yi wa Jabbari sassauci domin a yanke ma ta hukuncin dauri a gidan Yari.

Amma dangin ba su amince da sassaucin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.