Isra'ila-Falesdinu

Falasdinu ta ce rufe Masallacin al-aqsa da Isra'ila ke yi zai tada Yaki a Duniya

RFI Hausa

Kasar Isra’ila ta sake bude Masallacin al-aqsa na Kudus bayan Sao’I da rufe shi, da kuma kiraye-kirayen da kasashen Larabawa da Amurka suka yi akan bukatar yin hakan domin kaucewa tashin hankali 

Talla

Dama dai shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya yi kashedin cewar ba yanda za'a yi al'ummar Falasdinu su bar Isra'ila ta rufe Masallacin, kuma yin hakan sare-sarin tada fada ne a tsakanin al'ummar Musulmi da Yahudawan Duniya, ba a tsakanin Falasdinu da Isra'ila kurum ba.

Mai magana da Yawun jami’an tsaron Isra’ila Luba Samri ya shaidawa Kamfanin dillancin labarai na AFP cewar daga cikin dalilan sake bude Masallacin shi ne gudun barkewar tashin hankali a yau Jumu’a, sannan za’a hana mutanen da shekarunsu suka zarta 50 shiga wurin a yau Jumu’a.

Kasar Amurka da aka ce ta bukaci Isra’ila da ta bude Masallacin ta yi kira ga dukkanin bangarorin biyu da su hadiye fushi.

Amurkar haka ma ta yi kakkausar suka akan kisan da aka yiwa Yehuda Glick mai Takardun halascin zama dan kasar Isra’ila da Amurka.

Nan da kwana daya ne dai ake sa ran haduwar Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan wannan batu.

Tashin hankali tsakanin Isra’ila da Falasdinu dai ya ki ci ya ki cinyewa sakamakon yanda a baya Hamas da Fatah suka kulla kakkarfar dangantakar Diplomasiyya da karfin Soji, abinda isra’ila a nata haujin, ke yiwa hangen babbar barazana, musamman idan Kungiyar Hamas ta samu mulkin kasar Falasdinu a nan gaba.

Ko a babban taron Majalisar dunkin Duniya da aka gudanar a kasar Amurka a Watan da ya gabata, shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya yi kira akan dagawa Falasdinu Kafa ta kasance kasa mai cikakken ‘yanci, inda ma yake bayyana cewar lokacin samun hakan ya yi ga Falasdinu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.