Lebanon

An cafke Matar Baghdadi shugaban IS a Lebanon

Abou Bakr al-Baghdadi, Shugaban Mayakan ISIS da suka kafa sabuwar Daular Islama a Iraqi
Abou Bakr al-Baghdadi, Shugaban Mayakan ISIS da suka kafa sabuwar Daular Islama a Iraqi REUTERS/Social Media Website via Reuters TV

Jami’an tsaron kasar Lebenon sun kama daya daga cikin Matan Abu Bakr al Baghadadi shugaban Mayakan IS da ke da’awar Jihadi a Syria da Iraqi. An cafke matar ne da dansa a kan iyakar Lebanon da Syria.

Talla

Rahotanni daga Lebanon sun ce Matar ta amsa tambayoyi bayan Jami’an tsaro sun cafke ta kwanaki 10 da suka gabata.

A watan Yuni ne Baghdadi ya ayyana kansa a matsayin shugaban daular musulunci a yankin Syria da Iraqi da mayakansa suka kwace iko.

Iyalin na Baghdadi sun nemi shiga Lebanon ne daga Syria da takardun jabu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.