Philippines

Guguwar Hagupit ta yi ta'adi a kasar Philippines

Wasy 'yan kasar Philippines, lokacin da suke tserewa daga yankunan da guguwar
Wasy 'yan kasar Philippines, lokacin da suke tserewa daga yankunan da guguwar AFP PHOTO/TED ALJIBE

Mahaukaciyar guguwar Hagupit ta yi mummunan ta’adi a gabacin kasar Philippines, inda ta rusa gidaje da dama, tare da yin sanadin mutuwar mutane akalla uku. An bayyana cewa wannan ita ce guguwa mafi muni da ta abkawa Philippines a bana.

Talla

Mahaukaciyar guguwar ta Hagupit mai tafe da iska da ruwa ta tafi da gidaje tare da karya itatuwa da ma turakun wutar lantarki.

An bayyana guguwar a matsayin mafi muni da ta shafi Philippines a bana, inda take da karfi fiye da guguwar da ta shafi kasar a watan Yuli inda mutane 100 suka mutu.

Kodayake kafin zuwan guguwar Hagupit, mahukuntan kasar ta Philliphines sun dauki matakan kwashe mutanen da ke rayuwa a tsibirin Samar da ke gabacin kasar, don kaucewa tsanantar hasarar rayuka.

Wannan matakin kuma ya taimaka wajen tsirar da rayukan miliyoyan mutanen kasar, da suka kaucewa ta’adin da guguwar Haiyan ta yi a bara.

Kusan yanzu mutane miliyan guda guguwar ta shafi muhallinsu. Kuma har yanzu ba a iya tantance girman ta’adin da guguwar ta yi ba, saboda karfin iskan da guguwar ke tafe da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.