Saudi-Syria

Saudiya ta ba mutanen Syria Tallafi

Mutanen Syria a yankin Kobane suna karbar sadakar abinci
Mutanen Syria a yankin Kobane suna karbar sadakar abinci . REUTERS/Osman Orsal

Kasar Saudi Arabia ta bayar da taimakon Dala miliyan 52 don tallafawa ‘Yan gudun hijirar kasar Syria da ke fama da matsalar rashin abinci. Shugaban hukumar samar da abinci ta majalisar Dinkin Duniya Ertharin Cousin ta bayyana farin cikinta da matakin wanda ya kawo adadin taimakon da aka samu zuwa Dala miliyan 88.

Talla

Kasar Denmark da tafi kowace kasa bada agaji ta soki kasashen larabawa da jan kafa wajen bada na su taimakon.

Ofishin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya soki manyan kasashen duniya na nuna halin ko oho ga yawan adadin bakin hauren da ke mutuwa yayin da suke kokarin tsallaka teku zuwa kasashen Turai don neman abinci.

Yawancinsu kuma sun fito daga kasashen da ke fama da yaki irinsu Syria da kuma Eritrea inda mutane ke gujewa kuncin rayuwa a kasar.

Gwamnatin Kasar Spain ta ceto yan kasar Syria 408 da suka kwashe kwanaki 6 a cikin teku a kokarin sun a tsallakawa nahiyar Turai.

Cibiyar gudanar da binciken Spain yace mutanen da ke cikin jirgin ruwan na fama da tsananin yunwa da kishin ruwa lokacin da aka ceto su.

Tekun Mediterranean ya zama hanyar da dubban bakin haure ke amfani don tsallakawa nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.