Iraq

Dubban mutane sun bata a Iraqi

Mayakan IS da ke da'awar jihadi a Iraqi da Syria
Mayakan IS da ke da'awar jihadi a Iraqi da Syria REUTERS

Ma’aikatar kare hakkin dan adam a kasar Iraqi tace akalla mutane 2,700 ne suka bata sakamakon hare haren da Mayakan IS masu da’awar Jihadi suka kai a kasar Iraki, kuma an bayyana yawancin wadanda suka bace sojoji ne.

Talla

Rahoton Ma’aikatar ya yi nuni cewa yawanci wadanda gwamnati ta yi rijistar sun kunshi sojoji Dubu Daya da Dari Shida da Sittin kuma suna bakin aiki ne a yayin da ‘yan jihadin suka karbe sansaninsu a garin Tikrit watanni shida da suka gabata.

Mayakan IS sun kuma kama wasu firsunoni 487 da kuma wasu mutane 554 a wasu sassan kasar cikin su kuwa har da mata 38.

Wadannan alkaluman kamar yadda hukumar ke cewa an same su ne bayan ‘yan’uwan mutanen sun bayar da cigiyarsu da kuma sakamakon binciken wasu ma’aikata.
Hhukumar tace ga dukkan alamu wadanda suka batan yawansu zai haura adadin.

Hukumar tace kawo yanzu baa san makomar daruruwan mata ‘yan yazidi da ‘yan kungiyar ta IS ta kama tun a watan Satumba.

Kungiyar IS mai da’awar Jihadi don kafa daular Islama, tun bayyanarta, ta kaddamar da munanan hare-hare a kasar ta Iraqi tare da kashe mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.