Isa ga babban shafi
Indonesia-Malaysia

AirAsia: Matsalar yanayi ya kawo tsaiku

jirgi mai saukar Angulu a Teku domin aikin tsamo gawawwakin Fasinjan jirgin AirAsia
jirgi mai saukar Angulu a Teku domin aikin tsamo gawawwakin Fasinjan jirgin AirAsia Reuters
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Matsalar yanayi ya tursasawa masu aikin binciken gawawwakin Fasinjan Jirgin AirAsia 162 a tekun Java dakatar da aikin, a yayin da masu binciken suka fara nazarin dalilin da ya sa jirgin ya yi hatsari a teku.

Talla

Masu binciken sun yi nasarar tsamo gawawwakin mutane sama da 40 tare da wasu tarkacen jirgin AirAsia wanda ya yi hatsari bayan ya fito daga Surabaya na Indonesia zuwa Singapore a ranar Lahadi.

Mahukuntan Indonesia sun tabbatar da cewa takarkacen da aka tsamo a teku na jirgin AirAsia ne.

Yanzu haka mahukuntan Indonesia sun sanar da dakatar da bukukuwan sabuwar shekara domin juyayin wannan al’amari na hatsarin jirgin AirAsia.

Ma’aikatar tsaron Amurka tace za ta tura karin wani jirgin ruwa, don taimakawa a aikin laluben sassan jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.