AirAsia

Ana ci gaba da aikin neman tarkacen jirgin AirAsia

Masu aikin binciken Jirgin AirAsia da ya bata
Masu aikin binciken Jirgin AirAsia da ya bata REUTERS/Bagus Indahono

Yau Juma’a masu aiki neman sassan jirgin saman da ya yi hadari a kan tekun Java na kasar Indonesia, sun ci gaba da aikin, kuma suna gab da kaiwa inda lamarin ya faru. An dakatar da aikin neman Jirgin ne saboda matsalar Yanayi a tekun Indonesia

Talla

Zuwa yanzu an sami gawarwaki 16, da karin sassan jirgin, na kamfanin AirAsia, a aikin da kwararru daga kasashen Faransa da Singapore ke amfani da na’urori, a yunkurinsu na gano na’urar da ke nadar bayanan cikin jirgin.

Da sanyin safiyar ranar Lahadi jirgin ya bace, dauke da mutane 162, a lokacin da ya ke ratsa tekun Java akan hanyarsa daga Surabaya zuwa Singapore.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.