Indonesia

An gano manyan tarkacen jirgin AirAsia a teku

Jami'an Indonesia suna kwaso tarkacen jirgin AirAsia da aka gano a tekun Indonesia
Jami'an Indonesia suna kwaso tarkacen jirgin AirAsia da aka gano a tekun Indonesia REUTERS/Darren Whiteside

Masu aikin binciken jirgin AirAsia sun gano manyan takarcen jirgin a cikin tekun Indonesia da ya tarwatse a makon jiya. Babban Jami’in masu aikin ceto a kasar Indonesia yace an gano manyan tarkacen jirgin guda biyu a teku a daren juma’a, yayin da kuma ake ci gaba da neman sauran sassan jirgin tare da gano dalilin da ya sa jirgin ya yi hatsari.

Talla

Tuni Kamfanin AirAsia ya bayyana dakatar da zirga-zirga daga birinin Surabaya zuwa Singapore hanyar da jirginsa ya yi hatsari a ranar Lahadin da ta gabata dauke da fasinja 162.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.