Pakistan

Taliban: Pakistan ta yi alkawalin ladar kudi

Mulla Fazlullah shugaban Kungiyar Taliban a Pakistan
Mulla Fazlullah shugaban Kungiyar Taliban a Pakistan longwar journal

Gwamnatin Pakistan ta ce za ta bayar da ladar dala dubu dari ga duk wanda ya taimaka da bayanai domin cafke shugaban kungiyar Taliban da ke kasar Mullah Fazlullah. Gwamnan lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke kusa da iyakar kasar da Afghanistan inda aka fi samun yawaitar hare-haren Taliban, ita ce za ta bayar da kudin.

Talla

Bayan wani hari da kungiyar ta kai har aka samu asarar rayukan mutane sama da dari, gwamnatin Pakistan ta yi alkawalin yin amfani da duk iya karfinta domin murkushe Mayakan Taliban.

A cikin watan Disemba ne kungiyar Taliban kashe mutane 141 a makarantar ‘yayan sojojin da ke Peshawar, kuma cikinsu akwai yara 132.

An danganta al’amarin a matsayin mafi muni daga cikin hare haren da Taliban ke kai wa a Pakistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.