Syria

‘Yan adawan Syria sun yi watsi da goron gayyatar Rasha

Shugaban Syria, Bashar al-Assad
Shugaban Syria, Bashar al-Assad REUTERS/SANA/Handout via Reuters

Shugaban gamayyar kungiyar adawa a kasar Syria ta sa kafa ta shure amsa goron gayyatar shiga tattaunawar sulhu da gwamnatin Syria karkashin inuwar Rasha domin maido da zaman lafiya a kasar.

Talla

Sabon jagoran gamayyar kungiyoyin ‘yan adawa Khaled Khoja ya bayyanawa taron manema labarai a Istanbul cewa sam tsarin Rasha banda su a ciki.

Ya fadi cewa abin da kawai zai sa su zauna a tebur din sasantawa da jami’an Gwamnatin Shugaba Bashar Assad na Syria shi ne batun kafa Gwamnatin riko da za a ba ta dukkan karfi yin yadda ta ke so.

Rasha wadda ke sahun gaba wajen mara wa Shugaba Bashar Assad baya na ta hakilon ganin ta maido da da sasantawa tsakanin bangaren Shugaba Bahsar Assad da kuma bangaren ‘yan tawayen kasar.

Ta gayyaci wakilan ‘yan adawa 28 domin tattaunawan sulhu a cikin wannan watan.

Sabon shugaban gamayyar ‘yan adawan dai rikakken dan adawa ne, wanda ya sha gwagwarmaya domin yanzu haka yana gudun hijira ne a Turkiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.