Indonesia

An gano jelar jirgin AirAsia a tekun Indonesia

Sassan tarkacen Jirgin AirAsia da aka tattaro a tekun Indonesia
Sassan tarkacen Jirgin AirAsia da aka tattaro a tekun Indonesia REUTERS/Darren Whiteside

Hukumomin Kasar Indonesia sun ce sun gano jelar jirgin AirAsia mai lamba 8501 da ya tarwatse a tekun Java bayan kwashe kwanaki 11 ana aikin ceto. Shugaban aikin Bambang Soelistyo yace sun yi nasarar samo sashen jirgin da suka dade suna nema.

Talla

Jelar Jirgin tana dauke da bakin akwati da ke kunshe da na’urorin sadarwar jirgin. Kuma samun jelar zai taimaka wa masu aikin binciken jirgin gano dalilin hatsarin.

Gawawwakin mutane 40 aka tsamo daga tekun Java amma ana tunanin sauran fasinjan jirgin suna can makale a gangan jirgin.

Jirgin ya tarwatse ne a Teku dauke da mutane sama da 160 akan hanyrsa daga garin Surabaya na Indonesia zuwa Singapore.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.