Saudi

Saudiya ta bulale wanda ya ci zarafin Musulunci

via dailymail

Gwamnatin kasar Saudiya ta fara zartar da hukuncin bulala 1,000 a bainar Jama’a ga mutumin da ya ci zarafin addinin Islama a Intanet. A yau Juma’a an yi wa Raef Badawi bulala 50 kafin makwanni masu zuwa ya kammala shan sauran bulalar.

Talla

Kotu ta kuma yanke ma sa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.

Amurka da kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International sun bayyana adawa da hukuncin.

An zartar wa Badawi hukuncin ne bayan kammala Sallar Juma’a a Masallacisn Al Jafali a birnin Jedda a bainar Jama’a.

Saudiya kuma ta ci tarar Badawi kudi Riyal Miliyan guda tare da haramta ayyukan kungiyarsa da ke yada manufofin cin mutuncin Musulunci a shafin Intanet.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.