Qatar

Manyan Malaman Musulmi sun la’anci Mujallar Charlie

Youssef al-Qaradawi, Shehin Malamin Addinin Islama.
Youssef al-Qaradawi, Shehin Malamin Addinin Islama. AFP PHOTO/Karim JAAFAR

Kungiyar Masana addinin Musulunci ta duniya karkashin jagorancin shehin malamin kasar Masar Al-Qaradawi, ta la’anci ayyukan Mujallar Cherlie bayan Jaridar ta sake wallafa sabon zanen mutum da ta danganta da Manzon Allah SAW.

Talla

Malaman sun ce wannan mataki ne da ke kokarin tunzura musulmi.

A cikin wata doguwar sanarwa, Shehin Malami Yusuf al-Qaradawi, yace babu wata hujja da wani zai yi zane ya dangata da Manzon SAW.

Kungiyar ta kunshi masana ilimin addinin Islama a akidar Sunni da Shi’a da sauran akidu a duniya.

Masanan sun ce wannan alamu ne da ke nuna kasashen yammaci suna kyamar addinin Islama. Sannan mataki ne da zai kara tunzura musulmi musamman masu tsaurin ra’ayi.

Al-Qaradawi, mai shekaru 88 babban Malami ne a kasar Masar, amma yanzu yana rayuwa ne a kasar Qatar bayan hambarar da gwamnatin ‘Yan uwa Musulmi ta Muhammed Morsi.

Haka kuma Shehin Malamin addinin Islama Sheikh Ahmed al-Ghamedi yace sake wallafa zanen kuskure ne.

A cewar Shiekh Ghamedi, ya dace duniya ta fahimci cewa Annabi Issa da Musa AS dukkaninsu manzannin Allah ne, don haka kuskure ne wani ya mayar da su abin wasa.

Kasashen Musulmi da dame ne suka yi allawadai da Mujallar Charlie da suka hada da Iran da Qatar da Masar da Turkiya.

Dubban Musulmi ne suka shiga zanga-zanga a kasar Philipphines domin nuna adawa da Mujallar Charlie.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.