Isa ga babban shafi
Indonesia

An gano wasu gawarwakin Fasinjan AirAsia

Wasu tarkacen Jirgin AirAsia da aka tsinto a teku
Wasu tarkacen Jirgin AirAsia da aka tsinto a teku REUTERS/Darren Whiteside
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
Minti 1

Sojin ruwan kasar Indonesia sun gano gawarwakin mutane 6 wadanda aka tabbatar da cewa na fasinjojin jirgin saman AirAsia ne da ya tarwaste a tekun Java. Yanzu gawarwakin mutane 59 kenan daga cikin 162 aka gano, wadanda suka mutu sakamakon fadowar jirgin.

Talla

Jirgin ya tarwaste ne a Teku bayan ya taso daga garin Surubaya na Indonesia zuwa Singapore a ranar 28 ga watan Disamban da ya wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.