Saudiya

Tarihin Sarki Salman na Saudiya

Sarki Salman na Saudiya
Sarki Salman na Saudiya REUTERS/Saudi Press Agency/Handout via Reuters

Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud Shi ya gaji Sarki Abdallah da ya rasu a yau Juma’a kuma shi ne Da na 25 ga mahaifinsu Sarki Abdul’aziz bin saud na Saudi Arebiya.

Talla

An haifi Sarki Salman a ranar 31 ga watan Disemaban shekarar 1935, kuma shi ne Da na shida ga Sarki Abdul’aziz da ya zama sarkin Saudiya bayan mutuwar mahaifinsu.
Mahaifiyar Sarki Salman guda da tsohon Sarki Fahd wanda ya rasu a 2005.

Sarki Salman yana da shekaru 20 ya karbi mukamin Gwamnan birnin Riyadh tun daga shekarar 1963 har zuwa 2011 Wanda ya raya birnin da ayyukan ci gaba.

Bayan rasuwar Yarima Sultan ne Sarki Salman ya rike mukamin Ministan tsaron Saudiya a shekarar 2011.

A watan Yunin 2012 ne aka nada shi Yarima mai jiran gado bayan rasuwar Yarima Nayef, kuma tun daga lokacin ne ya fara tafiyar da harakokin diflomasiya tsakanin Saudiya da kasashen yammaci da kuma yankin Asiya.

Yanzu kuma babban kalubalen da ke gaban Sarki Salman shi ne daidaita tattalin arzikin Saudiya saboda faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.