Pakistan

Amurka ta kai hari wa kungiyar Taliban ta Pakistan

dronewars.net

Harin da Kurman Jirgin yakin kasar Amurka ya kai a wani yanki na Islamabad na kasar Pakistan, ya hallaka wasu mutane 6 da ake zaton sojin sa kai ne

Talla

Harin dai an kai shi ne da manufar afkawa wani Gini na ‘yan kungiyar Taliban da ke a Arewacin Waziristan, inda aka ce nan ne Malabar ‘ya’yan kungiyoyin al-Qaeda da Taliban.

Wani babban jami’in tsaron kasar Amurka ya ce kurman Jirgin yakin na Amurka dai ya harba Makami mai linzami ne guda biyu a kan Gidan da ake zaton na ‘yan Taliban ne a Arewacin Waziristan, ya kuma kashe akalla mutane 6.

Wannan harin da kasar Amurka ta kai dai ya dada haddasar fargabar cewar mai yuwa ne kasar ta Pakistan na ci gaba da hada Hannu da Amurka ne a wannan fadan da suke da kungiyar al-Qaeda.

Ana iya lura da hakan ne kuwa ganin yadda Pakistan ta musanta raderadin da ake cewar harin da Amurka ta kai, keta hurumin kasar ta Pakistan ne.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.