Isra'ila

Hizboullah ta kai hare-haren ramuwar gayya ga Isra’ila

Magari ya yakiteketea kwa moto karibu na kijiji cha Ghajarkwenye mpaka wa Israel na Lebanon, Januari 28 mwaka  2015.
Magari ya yakiteketea kwa moto karibu na kijiji cha Ghajarkwenye mpaka wa Israel na Lebanon, Januari 28 mwaka 2015. REUTERS/Maruf Khatib

‘Ya’yan kungiyar Hezbollah su kai hare-hare kan wasu yankunan da Sojin Isra’ila ke tsare da su a wani yanki da ke kusa da kasar Lebanon

Talla

Isra’ila ta mayar da martani wanda kuma hakan ya hadasa mutuwar wani sojan kasar Spain.

Isra’ila ta mayar da martani a hare-hare da ‘yan kungiyar Hezbollah suka kai a wani yanki da ke kan iyaka da kasar Lebanon, martanin da ya yi sanadiyar mutuwar sojan kasar Spain da ke aiki da rudunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar dunkin Duniya.

Firaiministan Isra’ila Benjamin Nethanyahu da kaukausar murya ya tabbatar da cewa sojin isra’ial za su mayar da martani bayan kisan sojinta biyu da ‘yan kungiyar Hezbollah suka aikata a harin da suka kai a gonakin da ke garin Chebaa.

Isara’ila ta harba wani makami mai cin dogon zango zuwa yankin na falesdinawa, kuma shaidun gani da ido sun bayyana cewar falesdinawa da dama ne suka samu rauni, yayin da a dai bangaren, Falasdinawa da dama ne suka fito domin nuna bacin ransu a gaban Ofishin Majalisar dunkin Duniya da ke a yankin.

Zanga-zanagar da ke biyowa bayan soke tallafin da aka warewa kasar Falasdinu domin gina sabbin Gidaje, tun bayan hare-haren da Isra’ila take a yankin a watan Nuwamban shekarar 2014.

Sama da falesdinawa 200 ne dauke da sakonnin batanci zuwa Majalisar dunkin Duniya, suka nemi kutsa kai cikin ofishin da ke yankin zirin Gaza.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.