Thailand

Ana ci gaba da kama jami'an Gwamnati a Thailand

Sabon firaministan Thailand,Janar Prayuth Chan-Ocha
Sabon firaministan Thailand,Janar Prayuth Chan-Ocha REUTERS/Chaiwat Subprasom

A Thailand , yau juma’a wata hukuma da ta lashi takobin yaki da fataucin mutane, ta tabbatar da kama wasu mutane tareda gurfanar da wasu jami’an gwamnatin kasar da dama, da suka hada da jami’an ‘yan sanda da jami’in sojan ruwa, saboda zargin su da hannu a fataucin mutane.

Talla

Dama an dade ana ganin kasar a matsayin wani yankin da ake bautar da mutane, kuma ana zargin jami’an gwamnatin da hannu, da rashin yin abida ya dace don kawo karshen lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.