Jordan

Jordan ta gindaya sharudda kamin sakin Macen kungiyar ISIS

Isis da  mutumin da suke garkuwa da shi
Isis da mutumin da suke garkuwa da shi

Hukumomi a kasar Jordan sun sanar da cewa har yanzu suna jiran shaidun dake nuna cewa matukin jirgin saman da mayakn kungiyar ISIS suka yi barazanar hallakawa, yana cikin koshin lafiya.

Talla

Kungiyar ta ISIS ta yi barazanar hallaka Maaz al-Kassasbeh kafin faduwar ranar jiya Alhamis, in hukumomin birnin Amman basu saki wata mace ‘yar kunar bakin wake ba, da ake tsare da ita a gidan yarin kasar.
Hukumin na Jordan sun ce sai sun tabbatar matukin jirgin na nan da ranshi kafin su saki matar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.