Saudi

Sarki Salman ya kafa sabuwar Gwamnati a Mali

Déclaration du nouveau roi d'Arabie saoudite, Salman, le 23 janvier 2015. à Riyad.
Déclaration du nouveau roi d'Arabie saoudite, Salman, le 23 janvier 2015. à Riyad. REUTERS/Saudi Press Agency/Handout via Reuters

Mai Alfarma sabon Sarkin Saudiyya Salman bin Abdel-Aziz ya sanar da wasu jeri sauye-sauye a Gwamnatin kasar ta Saudi Arebiya, inda dakatar da biyu daga cikin ‘ya’yan tsohon Sarkin da ya gada, wato marigayi Sarki Abdallah bin Abdel-Aziz daga mukaman da suke rike da su a zamanin mahaifinsu

Talla

Da yammacin jiya Alhamis ne Sarki Salman bin Abdulaziz al-Saud, ya gabatar da sabon tsarin Gwamnatin da zai mulka inda ya kawar da Dan tsohon Sarki yarima Khalid bin Bandar daga mukamin Babban mai kula da harkokin kasar Saudiyyan.

Mako daya kenan dai da sabon Sarkin ya hau Karagar mulkin kasar, bayan mutuwar tsohon Sarki mai shekaru 90, saboda laulayin ciwo da ya yi fama da shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.