Jordan

Jordan za ta mayar da zazafan martani kan mayakan ISIL

Sadfi al-Kassesbeh, mahaifin direban jirgin yakin Jordan da aka kashe
Sadfi al-Kassesbeh, mahaifin direban jirgin yakin Jordan da aka kashe REUTERS/Muhammad Hamed

Sarkin kasar Jordan Abdallah na biyu wanda ya katse ziyarar aikin da ya kai kasar Amurka bayan da mayakan da ke da’awar jihadi suka kashe wani direban jirgin yakin kasar mai suna Moaz Kasasbeh, ya bukaci jami’an tsaron kasar su kara damara domin mayar da martanin da ya dace.

Talla

A lokacin wani tsron gaggawa da manyan jami’ansa, sarkin ya kuduri aniyar mayar da zazzafan martani kan mayakan na ISIL bayan wannan kisa da suka yi ta hanyar kona direban jirigin da rayuwarsa a cikin keji.

Hakazalika hukumomin na Jordan ya ce kasar ba ta da niyyar ficewa daga cikin rundunar kawancen kasashen duniya da ke yakar dakarun da ke da’awar jihadi a Syria da kuma Iraki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI