Saudiya

Saudiya ta fille kan wani Ba’indiye

Ana Zartarwa wani hukuncin Bulala a Saudiya
Ana Zartarwa wani hukuncin Bulala a Saudiya via dailymail

Hukumomin kasar Saudi Arabiya sun fille kan wani Ba’indiye da yi amfani da gatari ya yi kisan kai, da kuma dan kasar Pakistan da aka samu da laifin fataucin miyagin kwayoyi. Sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta fitar, ta nuna cewa an sami Vijay Kumar Saleem dan Indiya da laifin daba wa wani dan kasar Yemen gatari a kai, lokacin da suke rigima a wajen aiki, kuma an zartar mi shi kukuncin kisa ne a birnin Riyadh.

Talla

Hafiz Wifaq Rasoul Shah da aka samu da fataucin hodar Ibilis, an zartar mi shi da hukuncin ne a garin Makkah.

Hukuncin shi ne na 34 a jerin wadanda aka zartar wa hukuncin kisa cikin kasar cikin wannan shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.