Iran

Iran ta ce ba za ta fada Gadar Zaren kasashen Duniya ba

REUTERS/Evan Vucci/Pool

Jagoran juyin juya halin musuluncin kasar Iran Ayotallah Ali Khamene’e ya ce tawagar kasar da ke jagorantar tattaunawar Nukiliya da kasashen duniya ba za ta fada cikin gadar zaren da kasashen ke shirya mata ba

Talla

A jawabinsa gaban wakilan majalisar kolin kasar Khomene’e ya ce Iran ta san abinda ta ke yi, don haka ba za ta bari a yi mata sakkiyar da ba Ruwa ba.

Wannan dai ya biyo ne bayan wasikar da ‘yan jami’iyyar Republican a kasar Amurka suka aika wa shugaba Barack Obama ne, inda suka bayyana cewa ba za su amince da kulla yarjejeniyar Nukiliya da Iran ba kamar yadda suka aikawa Iran irin wannan wasikar.

Tattaunawar Iran da manyan kasashen Duniyar dai na fuskantar babban kalu-bale, lura da yadda Iran ta kafe akan matsayinta, a yayin da kassahen Duniyar kuma suka kasa amincewa Iran akan kallon da suke mata na babban kalu-bale nan gaba.

Ko a baya bayan nan ma kasar Isra’ila ta bayyanawa Duniya cewar sai ta yi makarkashiyar lalata tattaunawar da Iran har ma tana gargadin Amurka da sauran kasashen Duniyar da cewar su yi hattara da bai wa Iran aminci ko kalilan.

Iran dai ta ce da kyakkyawar niyya take aikin sarrafa Uranium, kuma domin inganta jin dadin rayuwar al’ummarta, amma Isra’ila ta ce bata yarda ba.

Isra’ila dai na bukatar lallai kassahen Duniyar su tilasta Iran dakatar da aikin sarrafa Uranium, domin hart a kai fagen an yi sa-in-sa tsakanin Isra’ila da Amurka dangane da wannan batu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.