Afghanistan

Wani Hari ya kashe 'Yan Sanda a Afghanistan

AFP PHOTO / Noorullah Shirzada

Jami’an ‘Yan Sanda Kasar Afghanistan bakwai ne suka rasa rayukansu, akan hanyarsu ta zuwa karban albashi sakamakon wani hari da ake zargin ‘Yan Kungiyar Taliban ne suka kaddamarwa jami’an a arewacin Kasar

Talla

Hukumomin yankin Dashti na kasar, sun shaidawa kamfanin dillacin labaran faransa cewa, kimanin jami’an ‘Yan Sanda 30 ne harin ya ritsa dasu a lardin Kunduz, kuma suna kan hanyarsu ce ta zuwa lardin Takhar,inda zasu karbi albashin.

Kawo yanzu, babu wata kungiya da ta yi ikirarin farmakin, to sai dai ana zargin Kungiyar Taliban, sakamakon kaurin sunan da ta yi na haifar da rikice rikice, kuma kimanin shekaru 13 kenan da Afghanistan ke fama da matsalar Taliban.

A watan fabairun daya gabata, Kungiyar ta kashe jami’an ‘Yan Sanda Shida aYankin Maiwand dake kudancin lardin Kandahar, yayinda tuni, Kungiyar tsaro ta NATO da kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiya a kasar a watan Disamban daya wuce, sai dai ta bar tsirarun jami’anta dan horar da jami’an tsaron Afghanistan 350,000, da ake sa ran sune zasu kawo karshen Taliban.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.