Philippines

Guguwar Noul mai karfin gaske ta nufi arewacin kasar Philippines

Wasu mutanen da guguwar Hagupit ta yiwa ta'adi kwanakin baya, a kasar Philippines.
Wasu mutanen da guguwar Hagupit ta yiwa ta'adi kwanakin baya, a kasar Philippines. REUTERS/Erik De Castro

Yau Lahadi aka kwashe fiye da mutane dubu 1 daga gidajensu a kasar Philippines, sakamakon guguwar Noul, da ta nufi arewacin kasar, kuma take barazanar haifar da ambaliyar ruwa irinta tsunami da zaftarewar kasa. Hukumomin gwamnatin kasar sun ce tafiyar da guguwar ke yi ta dan sassauta, amma zuwa yanzu ta kara zuwa fiye da KM 200 a kowace sa’a, kuma ana tunanin zata kaiga tsibirin Luzon yau da rana ko da maraice.A kowace shekara kimanin na’ukan guguwa 20 ne ke afkawa kasar ta Philippines, kuma da dama daga ciki suna sanadiyyar rayukan jama’a.