An fatataki mayakan ISIL da ke kokarin shiga Palmyra
Wallafawa ranar:
Dakarun kasar Syria sun yi nasarar fatattakar mayakan ISIL masu da’awar jihadi bayan mayakan sun yi yunkurin kama garin Palmyra mai dadaden tarihi.Dakin addana kayyakin tarihi na Palmyra na da matuka daraja a Gabas ta Tsakiya.
Mayakan Isil sun isa yankin ne a ranar asabar inda suka kwace garin Tadmur da niyara kai hari a dakin tarihin sai dai kuma dakarun gwamnati sun yi nasarar fatatakarsu kafin su isa dakin
Shugaban gidan tarihin Mamoun Abdoukarim ya bayana matukar kaduwarsa sakamakon harin da ISIL suka kai yankin inda yace duk da cewa dakarun kasar sun yi nasarar korasu, har yanzu suna zama ne cikin fargaba. kuma har yanzu mayakan na cigaba da kasancewa a wajen garin
Nasarar da dakarun gwamnatin Syria suka yi ya biyo bayan munmunar gumurzu tsakanin su da mayakan al’amarin da ya janyo asarar rayukan mutane akalla dari uku a kwanaki hudu da aka kwashe ana gwabza fada
A baya kungiyar ISIL mai da’awar kafa daular Islma ta kai hare hare akan dakunan ajiyar kayan tarihi a kasar Iraq inda suka lalata kayyakin da suke dangantawa da gumaka wanda acewarsu ya sabawa addinin islama
Kawo yanzu mutane sama da dubu daya ne suka rasa rayukansu sakamakon hare haren mayakan ISIL a kasar ta Syria
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu