Japan

Japan na nazarin samar da ban-daki a Lifta

Ban-daki na zamani
Ban-daki na zamani Getty Images/Flickr Open/Rudolf Vlcek

Gwamnatin Kasar Japan na tunanin samar da ban-daki a cikin na’urar Lifta da ke jigilar mutane daga kasa zuwa saman dogayen benaye tare da samar da ruwan sha a ciki. Matakin ya biyo bayan yadda wasu mutane suka makale a cikin na’urar na dogon lokaci ba tare da samun ruwan sha ba ko inda za su biya bukatarsu, lokacin da aka samu girgizar kasa a ranar Assabar.

Talla

Tuni aka gudanar da taro tsakanin ma’aikatar da ke kula da gine gine da kuma masu aikin gina na’urar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI