Indiya

Indiya za ta fara bada tukuicin bahaya a makewayi

Firiya Ministan Indiya Narendra Modi
Firiya Ministan Indiya Narendra Modi Reuters/路透社

Majalisar Hukumar yankin Ahmedabad da ke Indiya ta yanke shawaran bada kudi ga duk wani mazaunin yanki da ya yi bahaya a makewayi, maimakon dabi’ar 'yin fitsari ko najasa a bainan Jama’a.Matakin na zuwa ne domin marawa matakin Gwamnati Firiya Minista Narendra Modi baya, a kokarin sa na chusa tsabta cikin Jama’a.

Talla

Majalisar yankin na Ahmedabad ta tsaida biyan duk mutum daya kudin kasar Rupee 1, idan har mutun ya yi amfani da makewayi, duk lokacin da ciki ya murda ko kuma akaji yin bawali.

Bhavik Joshi wani Jami’in lafiya yankin ya ce daukan wannan matakin ya zama wajibi domin hana al'adar mutan yankin, na kin yin amfani da makewayi idan akaji bukatar yin haka.

Jami’in lafiyan yankin ya ce yanzu haka suna da makewayi 67, da aka gina domin gwaji saboda Jan ra’ayin jama’a, su rika kaunar makewayi maimakon yi a bainan Jama’a, kuma idan har akaga anyi nasara, to ko shaka babu za’a gina makewayi 300 na amfani.

Wasu bayanan na cewa akasarin Jama’a kasar Indiya na kyamar makewayi sai dai kawai a yi a sararin Allah ta Allah.

Kamar ma yadda wani kididiga ke nunawa kusan rabin mutan kasar Indiya, wato mutane miliyan 594 basa kaunar shiga bahaya sai dai a yi a bainan Jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI