WHO ta gargadi Koriya ta Arewa game da cutar MERS
Wallafawa ranar:
Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi ga hukumomin kasar Koriya ta Kudu na gani sun karfafa matakan fadakar da al’uma kan cutar nan ta MERS mai kama da mura, dake da saurin kisa.Hukumar lafiyan ta kuma bayana matukar damuwar ta ga hukumomin kasar Koriya ta Kudu dangane da biris da suka yi, wajen bada kulawar data dace, don magance yaduwar cutar a kasar.
Hukumar ta WHO ta gabatar da kwararan shedun dake nuna cewa bayan kasar Saudi Arabiya, cutar ta yi sanadiyyar rasa ran mutane da dama a Koriya ta Kudun.
Hukumar ta kuma yi kira ga sauren kasshen Duniya, da su hada karfi da karfe, wajen yakar cutar ta MERS.
Wani mai Magana da yawun hukumar, ya bayana ceewa za su bayar da shawarwari na gari ga kasar ta Koriya, tareda kebe wa jami’an kiwon lafiya lokaci da ma kayan aiki na musaman wajen yakar wanan cuta.
Yayin wata ganawa da manema labaru a farkon wannan makon, Shugabar kasar ta koriya Park Guen Hye ta bukaci daukaci ‘yan kasar da sun yi taka tsan tsan, tareda kiyayewa dama bin umurni jami’an kiwon lafiya dangane da wanan cuta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu