Falasdin-Isra'ila

Falasdinu ta shigar da karar Isra'ila a Kotun duniya

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas AFP/Abbas Momani

Bayan samu shiga a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC a cikin watan Afrilu da ya gabata a yau Hukumomin Falasdinu, sun shigar da karar karon farko a kan Isra'ila inda su ke tuhumar ta da laifukan yaki a yankin zirin Gaza wanda aka yi a cikin shekarar bara.Wannan dai na zuwa ne a yayin da Isra'ila ke cigaba da nuna kin jinin Falasdin na amincewa da ita a Matsayin kasa.

Talla

Hukumomin Falasdinu sun ce suna da shaidun da za su gabatar a gaban Kotun ICC wanda zai tabbatar da zarginsu a kan Isra'ila na karya dokokin shari’ar kasa da kasa da kuma aikata laifukan yaki.

Ministan harkokin wajen Falasdinu, Riyad al-Malik ya ce gabatar da shaidu zai kara fitowa duniya irin aika-aika da Isra'ila ta yi, da kuma wanke Hamas daga zargin da ake yi mata na aikata laifi a Gaza.

Sai dai kuma a wani rahotan da ta taba fitarwa Majalisar dinkin duniya, ta zargi dukanin bangororin Isra'ila da Falasdinu da laifukan yaki a Gaza.

Riyad al-Malik dai na cewa shigar da karar a ICC zai bankado da gaskiyar lamarin.

A ranar Assabar mai zuwa, masu gabatar da karar a kotu na ICC za su kai ziyara Isra'ila domin aiwatar da bincike mai zurfi a kan zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.