Isa ga babban shafi
Isra'ila-Gaza

Isra’ila ta kame jirgin kayan agajin Gaza

Isra’ila na ci gaba da fuskantar suka kan yadda ta ke muzgunawa Falasdinawa.
Isra’ila na ci gaba da fuskantar suka kan yadda ta ke muzgunawa Falasdinawa. REUTERS/Stefanos Rapanis
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

Sojojin Ruwan Isra’ila sun sanar da kame wani jirgin ruwan da ke dauke da kayan agaji zuwa Yankin Gaza don tallafawa Falasdinawa. Rundunar sojin kasar ta ce ba ta yi amfani da karfi ba wajen kama jirgin mai dauke da baki masu rajin kare hakkin bil Adama da ke rakiyar kayan agajin.

Talla

Cikin masu rakiyar har da tsohon shugaban kasar Tunisa, Moncef Marzouki, da wani Balarabe Dan Majalisar Israila da Bassel Ghattas da wani Dan Majalisar kungiyar kasashen Turai.

Firaminista Benjamin Netanyahu ya yabawa sojojin ruwan inda ya bayyana tawagar jiragen a matsayin munafunci tare da shiga yankin ta barauniyar hanya.

Isra’ila dai na ci gaba da fuskantar suka kan yadda ta ke muzgunawa Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.