China

Ana karancin Yara a Makarantu saboda dokar takaita haihuwa a China

China ta harmata haihuwar sama da yaro guda
China ta harmata haihuwar sama da yaro guda DR

China na fuskantar matsaloli na a rashin Yara kanana da kuma yawan tsoffi sakamakon dokar kasar na haramta haihuwar sama da yaro guda, al’amarin da ya sa makaratu suka bushe a wasu yankunan kasar saboda babu yaran da za a koyar.

Talla

Yankin Rudong da ya yi kaurin suna wajen dandakar mutane da kuma tilasta zubar da ciki na daga cikin Yankunan da matsalar ta fi kamari, inda yanzu haka makarantun Yankin suka koma kango saboda babu yaran da za suyi karatu.

Akasarin yaran da aka haifa a Yankin sun ta fi birane don yin ayyuka inda yanzu baya ga dattijai babu kowa a Yankin.

Bincike ya nuna cewar kasar China za ta samu raguwar ma’aikatan da ta ke da shi miliyan 915 yanzu, inda za su ragu da miliyan 40 a shekarar 2030 da kuma miliyan 60 a shekara 2050.

Kuma Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasin cewa zuwa 2050, kashi 30 na mutanen China za su haura shekaru 60.

Matsalar kuma za ta ci gaba da shafar matasa wadanda za su koma kula da tsoffi maimakon mayar da hankali ga ayyukan da ke gabansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.