Palestine

An sake bude kamfanin sadarwar Jawwal da aka rufe yankin Gaza

Kungiyar Hamas da ke iko a yankin Gaza na Palasdinu, a yau lahadi ta bayar da izinin sake bude kamfanin wayar sadarwa daya da ke yankin wanda aka rufe kwanaki biyar da suka gabata bisa zargin boye gaskiya domin kauce wa biyan haraji.

Gaza na Palasdinu a ranar 17 ga watan yuni
Gaza na Palasdinu a ranar 17 ga watan yuni RFI/Murielle Paradon
Talla

Sanarwa daga ofishin mai shigar da kara na gwamnati a Gaza Isma’il Jaber, ta ce an bayar da umurnin sake bude kamfanin sadarwar mai suna Jawwal, to sai dai ba a bayar da karin bayani game da dalilan sake bude shi ba.

Shi dai wannan kamfani, ya kasance daya tilo da ke bai wa mazaunan zirin na Gaza da yawansu ya kai milyan daya da dubu dari bakwai damar buga waya zuwa sassan duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI