Yemen

Yemen na fatan kulla yarjejeniyar tsaigaita wuta da Sallah

Shugaban kasar Yemen, Abdrabuh Mansur Hadi.
Shugaban kasar Yemen, Abdrabuh Mansur Hadi. AFP

Gwamnatin Kasar Yemen da ke iko daga kasar Saudi Arabia ta ce tana fatan kulla yarjejeniyar tsagaita wuta wanda za ta kai har lokacin da za’ayi bikin Sallar Eid el Fitr, bayan wani harin da ya kasha mutane akalla 40.

Talla

Shugaban kasar Abdrabuh Mansur Hadi ya ce suna tattaunawa da 'Yan tawayen Houthi da ke samun goyan bayan Iran dan kulla yarjejeniyar da za ta tabbatar da shirin.

Akasarin manyan biranen kasar da ke tsakiya da kudancin Yemen sun gamu da mummunar fadar da ake gwabzawa tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.