Isra'ila

Isra'ila ta sako wani mutum da take tsare dashi ba tare da hukunci ba

Yau lahadi hukumonin kasar Isra’ila sun sako wani BaPalasdinen da suke tsare dashi, da kuma yayi yajin kin cin abinci tsawon kwanaki 56. Khader Adnan ya shirya yajin kin cin abincin da ya kusa mutuwa ne, don nuna adawa da wani tsarin da kasar ta Isra’ila, inda ake tsare mutane har sa illa ma sha Allahu, ba tare da gurfana gaban kotu ba. 

Palasdinawa dake zanga zangar neman sako Khader Adnane
Palasdinawa dake zanga zangar neman sako Khader Adnane Reuters / Mohamad Torokman
Talla

Jam’ar kauyen su Adnan, dake kusa da birnin Jenin, sun masa tarba irin ta jarumi, inda aka yi ta wasan wuta, waskoki da daga tutocin kungiyar mayakan Islamic Jihad, inda wasu suka sanya rigunan dake dauke da hotunan Adnan.
An sako Adnan mai shekaru 37 mai dogon gemu ne yau kafin gari ya waye, a wani matakin da ake gani za a kawar da hankulan jama’a a kan sakin da a aka yi tunanin za ayi da rana.
Mai magana da yawun hukumomin gidan yarin kasar ta tabbatar da sakin, sai dai ba wani karin bayanin da tayi game da lamari.
A nata bangaren, kungiyar Islamic Jihad ta taya Adanan murna kan abida ta kira nasarar da ya samu, a fito na fito da hukumomin kasar ta Isra’ila.
Cikin Palasdinawa 5,686 da ake tsare dasu a gidajen yarin Isra’ial, 379 suna tsare a karkashin wannan tsarin da hukumomin Palasdinawa suka koka a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI