Egypt

Rundunar Sojan Masar ta sanar da kashe 'yan ta'adda 59 a yankin Sinai.

Shugaban kasar Masar Abdul-Fatah al Sisi a lokacin da ya ziyarci yankin Sinai
Shugaban kasar Masar Abdul-Fatah al Sisi a lokacin da ya ziyarci yankin Sinai REUTERS/The Egyptian Presidency/Handout via Reuters

A yau lahadi dakarun gwamnatin kasar Masar sun sanar da kashe mayakan jihadi 59 a yankin arewacin Sinai, bayan da a jiya rundunar sojan kasar ta sanar da kashe mata dakaru 7 a cikin wani harbin roka da aka yi kan wani shingen tsaron sojojin gwamnatin kasar dake yankin nan mai fama da tashe tashen hankulla na Sinai

Talla

A jiya assabar dakarun gwamnatin dake samun dafawar jiragen saman yakin kasar sun kai hare hare a maboyar yan ta’adda a yankuna 14 dake arewacin mashigin na sinai, inda suka bayyana kashe yan tsagera 59 kamar yadda kakakin rundunar sojan kasar ta Masar ya sanar a wata sanarwa a yau lahadi, inda ya kara da cewa sun kama mayakan jihadin 4 da rai a lokacin samamen

Kasar Masar dai na fuskantar hare haren mayakan jihadi a yankin mashigin Sinai, al’amarin da ya tilastawa gwamnatin kasar zage dantse wajen yin fito na fito da yan ta’addan, da ke ci gaba da tada hankulla da sunan addinin Islama a yankin gabas ta tsakkiya, tun bayan wani kazamin harin da suka kai a farkon wannan wata a yankin na Sinai, da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 200 tsakanin dakarun gwamnati da mayakan j-ihadin kungiyar ta Isis

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI