An yi barazanar hallakar Shugaban kasar Isra’ila

REUTERS/Ronen Zvulun

Jami’an Yan sandan Kasar Isra’ila sun fara gudanar da bincike game da kalaman da aka sanya a shafin Internet inda akayi barazanar hallaka Shugaban Kasar Isra’ila Reuven Rivilin, bayan  yin allawadai da harin ta’addancin da wani bayahude ya kaddamar, inda ya kashe wani karamin yaro Bafalasdinu.

Talla

A ranar Jumma’ar da ta gabata ne shugaba Rivlin ya yi allawadai da harin ta’addancin da wani bayahude ya kaddamar a kan wani gidan falasdinawa da ke kauyan Duma a yamma da kogin Jordan, harin da ya yi sanadiyar mutuwar wani karamin yaro da bai haura watannin 18 ba Ali Sa'ad.

Har ila yau harin ya matukar raunata iyayen yaran harma da wasu  'ya'yan nasu.

Shugaba Rivilin wanda ya nuna takaicin sa kan lamarin ya ce maharan sun zabi hanyar da Kasar harma da sauran yahudawa suka yi tur da ita, yayin da ya bukaci daukan kwararan matakai domin magance masu tsaurara ra’ayi.

Tuni dai mutanen kasar suka yi ta mayar da martini kan kallamansa, inda wadansu suka goyi bayansa, wadansu kuma suka aika masa da kalamai marasa dadi ta shafin  Facebook tare da tunatar da shi irin kisan da Falasdinawa suka yiwa yahudawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.