Isa ga babban shafi
Japan

‘Yan Sandan Japan sun cafke wani da ya yanka al’aurar kwarton Matarsa

'Yan Sandan Japan a Tokyo
'Yan Sandan Japan a Tokyo Reuters
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

‘Yan sanda a Japan sun cafke wani mutum da ya abka ofishin wani lauya da ke kwartanci da matarsa ya yanka Azzakarinsa da babban almakashi sannan ya zuba cikin ban-daki.

Talla

Rahotanni sun ce mutumin mai suna Ikki Kodukai dan shekaru 24, ya fusata ne kan kishin Matarsa da ke kwartanci da Lauyan mai shekaru 42.

Kuma Kodukai ya tabbatar wa ‘Yan sanda cewa ya yanka Azzakarin tare da jefa shi a cikin Ban-daki na zamani.

Yanzu haka dai yana hannun ‘Yan sanda a Tokyo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.