Falasdin-Isra'ila

Falasdinawa na zargin Hamas da shiga tattaunar sirri da Isra’ila

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas AFP/Abbas Momani

Mahukuntan Falasdinawa a Ramallah sun zargi kungiyar Hamas da ke iko a Gaza da shiga tattaunawar sirri da gwamnatin Isra’ila kan shirin raba Yankunan Falasdinawa.

Talla

Ministan harkokin wajen Falasdinawa Riad al Malik ya ce akwai tattaunawar siri da bangarorin biyu ke yi, kuma sun kusa kulla yarjejeniyar tsagaita wuta na shekaru 8 zuwa 10, matakin da zai sa Israila ta cire shingen da ta sa a Gaza tare da da barin jiragen ruwa wucewa zuwa Cyprus.

Wata majiyar Hamas ta amince da cewar suna musayar ra’ayi da Isra’ila ta bayan-fage amma batun ayyukan jinkai kawai suka tattauna.

Sai dai kuma gwamnatin Isra’ila ta ce babu wata tattaunawa da ta ke yi da Hamas, kungiyar da ta danganta a matsayin ta ‘Yan ta’adda.

Kungiyoyin Hamas da Fatah ne dai ke shugabanci a yankunan Falasdinawa guda biyu, Gaza da gabar yamma da kogin Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.