Philippines

Guguwar Goni ta doshi Philippines da Taiwan

Wannan ne karo na shida da guguwa ke abkawa Philippines
Wannan ne karo na shida da guguwa ke abkawa Philippines REUTERS/Erik De Castro

Akalla mutane biyu aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da aka kwashe dubban mutane sakamakon wata guguwar Goni da ta doshi Philippines da Taiwan a yau Juma’a.

Talla

Mahukuntan Philippines sun ce wasu lebarori ne da ke aikin gini suka mutu bayan zabtarewar kasa da ta rufe rumfar da suke ciki a garin Itogon.

‘Yan sanda sun ce kimanin mutane 400 aka kwashe a yankunan da ke fuskantar ambaliyar ruwa.

‘Yan yawon bude kimanin 1,700 aka kwashe daga tsibirin Orchid a kasar Taiwan.

Hukumar kula da yanayi a Philippines ta yi hasashen cewa guguwar Goni za ta nufi Taiwan, wacce ita ce guguwa ta shida ta abka wa Philippines a bana.

Yanzu haka an  jinkirta tashin jirage a Japan saboda guguwar ta Goni da aka yi hasashen za ta doshi tsibirin Ogasawara da ke nisan kilomita 1,000 kudu da Tokyo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI